Kasashen Waje Sun Fara Fahimtar Tsananin Barazanar Kungiyar Boko Haram

Wani dan kasar Kamaru a Faransa ke daga tuta dake cewa, kawunan 'yan Kamaru yazo daya dangane da yaki da Boko Haram.

Cikin makoni masu zuwa, masana harkokin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro zasu yi wani taro a kasar kamaru, domin tattauna tsara dabarun yaki da ‘yan Boko Haram da tsara yadda sojojin hadin gwiwa wanda suka hada da kamaru, Chadi, Nijar, da jamhuriyar Benin, zasu gudanar aikin fatattakar yan Boko Haram.

To amma Najeriyar ta nace kan duk wasu matakai da za’a dauka wajen dakile kungiyar Boko Haram, a tabbata a baiwa fararen hular kasar kariya, domin rage jikatta yan fararen hular.

Wadannan bayanai, wani bangare ne na tarurrukan da aka yi a gefen taron kolin kungiyar tarayyar Afirka da akayi kwanaki a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, inda ministan harkokin wajen Najeriya, ambasada Aminu Wali ya jagoranci tawagar Najeriya.

Ya kuma bayyana jin dadin sa ga kokarin kungiyar tarayyar Afirka, wajen daukar matakai domin ganin an dakile aiyukan duk wata kungiyar ta’addanci dake barazana ga nahiyar Afirka.

Haka kuma ya yabawa rahoton kungiyar LCBC akan yunkurin da yankin ke yi, na yaki da Boko Haram. Ya kuma yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya daya hanzarta yin na’am da kudurin tura sojojin na hadin gwiwa da ake cewa MNJTF a takaice.

A karkashin jagorancin kasar Kamaru, kungiyar lekar asiri ta RIFU, tana kokari taimakawa wajen bada gudumawar yakar ta’addanci a yankin inji Wali.

Kasashe, wakilan kungiyar habaka tattalin arzikin Afrika ta yamma da ake cewa ECOWAS a takaice, sunyi wani taro a gefen taron kolin a karkashin shugabancin shugaban kasar Ghana John Dramini Mahama, wanda batun kungiyar Boko Haram ya kasance kan gaba a ajandar tattaunawar.

Gaba dayan su dai sun la’anci kungiyar yan ta’adan, wadda bata mutunta rayuwar mutane da kayansu, harma da kai hare hare kan fararen hula.

Sunyi alkawarin yin aiki da Najeriya don tinkarar kungiyar.

Ambassador Wali ya lura da yadda, daga baya Kasashen waje suka fahimci tsananin barazanar kungiyar Boko Haram, bama a yankin kawai ba, harma da wasu yankuna.