Ko A Yau Akayi Zabe Shugaba Jonathan Zai Koma Fadar Aso Villa – Inji Alhaji Isa Tafida Mafindi

Ziyarar John Kerry Zuwan Najeriya.

A yanzu da yake dukkan jam’iyyun siyasar Najeriya sun amince da ranar ashirin da takwas ga watan Maris, a zaman ranar da za’a gudanar da zaben shugaban kasa dana ‘yan majalisun Najeriya.

Manyan Jam’iyyun kasar guda biyu PDP da APC, duk sunce a shirye suke kuma kowa yana kwada kansa tare da harsashen samun nasara. Mukaddashin daraktan yada labarai na kamfen din shugaba Goodluck Jonathan, Alhaji Isa Tafida Mafindi yace su kam ko a yau a kace ayi zabe sun san shugaba Jonathan zai koma cikin fadar Aso Villa, ata bakin sa yace, “Siyasa kamar yaki take, kowa yana da irin makamin sa da irin shirye shiryen sa, to a bune da kowa zai bayyana abubuwan da sukayi, kuma babban abin da zan fada shine muna da zuciya na cewa duk lokacin da aka fito aka jefa kuri’a zamuci zabe. Kuma muna kan kamfen na bayyanawa ‘yan Najeriya cewa ga abubuwan da mukayi a zamanin da muke mulki.” Ya dai cigaba da cewa Shugaba Jonathan yayi tashoshin jiragen sama dana ruwa harma da jirgin kasa, ya kuma shinfida noma a kasar.

To sai dai takwarar aikin Alhaji Isa Tafida Mafindi PDP, itace Hajiya Naja’atu Mohammed ‘yar APC, tace, “Farko dai karya suke basuyi wadannan aiyukan da suka fadi ba, abin da yakamata dan Najeriya ya tambayi kansa shine menene ma aikin shugaban kasa? Aikin shugaban kasa na farko kamar yadda kundin tsarin mulki yace, shine kwamandan harsoshin Najeriya ga baki daya, shugaba Jonathan da bakin sa ya fito yace, shiba kwamanda harsoshin Najeriya bane, bai ma fahimci menene aikin sa ba, doka abin da tace shine a matsayin sa na kwamandan Najeriya yayi duk yanda zaiyi ya kare kasar daga waje ya kuma kare rai da lafiya da dukiyoyin al’umma a cikin gida.”

A yayin da jam’iyyun suke kara kaimin nasu, a wani gefe guda kuma babban abinda ke daukar hankulan jama’a yanzu shine rade radin dake kara karfi cewar fadar shugaban kasa tana son tilastawa Farfesa Attahiru Jega shugaban hukumar zabe ta INEC, daya tafi hutun dole kafin ran ashirin da takwas ga watan Maris, kuma bazai koma kan wannan kujera ba har izuwa karshen wa’adinsa a watan Yuni. Gwamnatin dai ta musunta wannan, amma kuma magoya bayan shugaba Jonathan cikin su harda Edwin Clark, suna daga cikin masu kiran da ama kori Jega, a kuma gurfanar dashi gaban kotu.

Saurari cikakken rahotan Ibrahim Alfa Ahmed.

Your browser doesn’t support HTML5

Mafindi da Naja'atu - 4'06"