Mai Martaba Sarkin Kano Yayi Kira Ga ‘Yan Siyasa Da Matasa

An dorawa Sabon Sarkin Kano, Mallam Sanusi Lamido Sanusi malafar sarki, da kuma bashi tagwayen masu Talatannan, a gidan gwamnatin Jihar Kano.

Mai martaba sarkin Kano Mallam Muhammadu Sunusi II, yayi kira ga ‘yan siyasa da suji tsoron Allah, su daina amfani da matasa don bangar siyasa domin su kansu ‘yan siyasar suna da ‘ya ‘ya, Sukuma dai na amfani da ‘ya ‘yan mutane a matsayin ‘yan banga. Haka suma matasan ya ja kunnensu da cewa duk abubuwan da ake saka su suke shan wahala, kuma su guji hakan.

Mai martaba ya fadi haka ne a wajen wani taron manema labarai da yayi a nan birnin Washington DC na Amurka, a lokacin da ya kawo wata ziyarar ganawa da jami’an wata masana’anta da ake cewa IGS a takaice.

A kokarin taimakawa mutane masu karamin karfi wajen samun gidajen da zasu iya biya, mai martaba sarkin Kano Mallam Muhammadu Sunusi na biyu, ya kawo ziyarar ne nan Amurka domin ganawa da masana’antar sarrafa harawar shinkafa da alkama wajen gina gidaje masu karfi, kamfanin dai na nan Amurka a birnin Fort Worth dake jihar Texas, bayan da mai martaba ya gana da jami’an wannan masana’anta sai kuma aka zagaya da shi domin ganin yadda masana’antar ke aiki.