A zauren matasa yau an tattauna ne kan shafin Blog, ta yadda za’a wayar wa da mutane kai kan muhimmancin shafin Blog na kan yanar gizo, dama amfanin sa ga al’umma harma da fadakar da matasa wajen nuna musu cewa kowa na iya bude shafin sadarwa na Blog wanda yake taimakawa jama’a wajen dogaro da kai, zakuma a iya amfani da shi wajen yin saye da sayarwa da harkoki da wadansu harkokin rayuwa.
Blog dai shafine da aka bude domin taimakawa mutanen dake harka da yanar gizo, wajen shiga da tallace tallace harma da yada wasu manufofi, kasancewar a wannan zamani mutane dayawa na samun labarai da duk wasu bayanai ta kan yanar gizo.
Ga duk matasan dake son bude shafin Blog abune mai sauki, kowa na iya shiga cikin yanar gizo da yin bincike kan yadda ake bude Blog, akwai bayanai daki daki da mutum zai iya bi domin mallakar shafin kansa, shafin na da matukar amfani wajen yin sana’a dabam dabam da yada manufofi ko ilamatar da jama’a kan wani batu mai muhimmanci.
Shawara ga matasa shine duk wanda ke son bude wannan shafi na Blog domin sana’a ko ilimantar da al’umma kuma bai san yadda zai yi ya bude wannan shafi ba, to ya sami wanda yake da ilimin fasaha, ana kuma iya hawa kan yanar gizo ayi bincike kan shafukan buncike da suka hada da Google, Yahoo, Bing da dai sauransu.
Saurari cikakkiyar tattaunawar matasan.